92:10To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
92:11Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).
92:12Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.
92:13Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
92:14Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
92:15Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa.
92:16Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
92:17Kuma mafi taƙawa zai nisance ta.
92:18Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.
92:19Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.
92:20Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
92:21To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).
93:1Inã rantsuwa da hantsi.
93:2Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
93:3Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
93:4Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
93:5Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
93:6Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
93:7Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
93:8Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
93:9Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
93:10Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
93:11Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).
94:1Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
94:2Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.