Ana lodawa...
1:1Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1:2Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
1:3Mai rahama, Mai jin ƙai;
1:4Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
1:5Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.
1:6Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
1:7Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.