78:1A kan mẽ suke tambayar jũna?
78:2A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?
78:3Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?
78:4A'aha! Zã su sani.
78:5Kuma, a'aha! Zã su sani.
78:6Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?
78:7Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?
78:8Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?
78:9Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?
78:10Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?
78:11Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?
78:12Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?
78:13Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?
78:14Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?
78:15Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?
78:16Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?
78:17Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.
78:18Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.
78:19Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.
78:20Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.
78:21Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.
78:22Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.
78:23Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.
78:24Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.
78:25Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.
78:26Sakamako mai dãcẽwa.
78:27Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.
78:28Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa!
78:29Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.
78:30Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.