74:48Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.
74:49Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya.
74:50Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.
74:51Sun gudu daga zãki.
74:52A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa
74:53A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.
74:54A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce.
74:55Dõmin wanda ya so, ya tuna.
74:56Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.
75:1Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba.
75:2Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba.
75:3Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?
75:4Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.
75:5Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.
75:6Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"
75:7To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).
75:8Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).
75:9Aka tãra rãnã da watã
75:10Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"
75:11A'aha! bãbu mafaka.
75:12zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
75:13Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
75:14Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
75:15Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).
75:16Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).
75:17Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.
75:18To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.
75:19sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.