78:31Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.
78:32Lambuna da inabõbi.
78:33Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna.
78:34Da hinjãlan giya cikakku.
78:35Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.
78:36Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.
78:37Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.
78:38Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.
78:39Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.
78:40Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"
79:1Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.
79:2Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.
79:3Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.
79:4Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre.
79:5Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.
79:6Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.
79:7Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.
79:8Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.
79:9Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.
79:10Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?
79:11"Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"
79:12Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"
79:13To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.
79:14Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.
79:15Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?
79:16A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?