80:41Baƙi zai rufe su.
80:42Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).
81:1Idan rãna aka shafe haskenta
81:2Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
81:3Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
81:4Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
81:5Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
81:6Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
81:7Kuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu.
81:8Kuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta.
81:9"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"
81:10Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
81:11Kuma idan sama aka fẽɗe ta.
81:12Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
81:13Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
81:14Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
81:15To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba.
81:16Mãsu gudu suna ɓũya.
81:17Da dare idan ya bãyar da bãya.
81:18Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
81:19Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
81:20Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
81:21Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.
81:22Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
81:23Kuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani.
81:24Kuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne.
81:25Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
81:26Shin, a inã zã ku tafi?
81:27Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
81:28Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
81:29Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.